12 Satumba 2025 - 21:47
Source: ABNA24
Ayatullah Sayyid Khatami: Isra’ila Za Ta Kai Hari A Kasashen Masar, Jordan, Bahrain, Da Saudiyya Idan Har Ta Samu Iko.

Limamin Juma'ar Tehran ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain, da Saudiyya da cewa yahudawan sahyoniyawa za su kai musu hari idan suka sami karfin iko, yana mai jaddada cewa hanyar tunkarar sahyoniyawan ita ce mayar da martani da karfi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Limamin sallar juma'a na Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana a cikin hudubar salllar juma’a cewa: "A matsayina na limamin juma'ar Tehran, ina cewa, ya kamata gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudi Arabiya su ji wanna maganar, idan har yahudawan sahyoniyawan suka samu iko, to za su kai hari gare ku, domin taken Netanyahu shine (kafa babbar Isr’ila) daga Tekun Nilu zuwa Tekun Furat domin yana kokarin kwace wasu sassan Masar da Jordan".

Limamin juma'ar Tehran ya kuma yi tsokaci kan harin da yahudawan sahyuniya suka kai kan Qatar da hedkwatar kungiyar Hamas a baya-bayan nan yana mai cewa: Halayen wannan gamnatin sahyoniyawan shine zubar da jini, kuma an kafata ne shekaru 80 da suka gabata ta hanyar zubar da jini. Ya kara da cewa: "Kada ku yi shakku cewa tabbas Amurka na da hannu a wannan aika-aika, sararin samaniyar kasar Qatar yana karkashin kulawar sansanin sojin Amurka na Al-Udeid, to ta yaya ba za su sani ba? Har wasu ma suna cewa ya zama wajibi sahyoniyawa su aiwatar da wannan mataki ai, kuma Trump ya ce ya yi bakin ciki ba don ta kai wa Qatar hari ba, sai don ta gaza kawar da jagororin Hamas, kuma shugabannin Hamas sun tsira." Khatami ya kara da cewa: kowa ya mayar da martani kan wannan wuce gona da iri na yahudawan sahyoniya, kuma wasu kasashen da suke rige-rige ga kulla alakarsu da sahyoniyawa suma sun yi Allah wadai da wannan aika-aika, a matsayina na limamin juma'ar Tehran, ina mai cewa, wajibi ne gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya su saurara! cewa: Idan wannan dan ta'addar ya samu iko, to kuma zai kai hari gare ku. Domin yana son kwace wasu sassan Masar da Jordan".

Ya kara bayyana cewa: "Hanyar tinkarar yahudawan sahyoniya ba ita ce yin kira da neman tallafin Majalisar Dinkin Duniya ko fakewa da yin amfani da cibiyoyi na kasa da kasa ba ne, Domin tana kai hare-hare a idon duniya, hanyar daya kawai  ita ce turmuza hancin sahyoniyawa. Dole ne su tattara dukkan sojojinsu su murkushe sahyoniyawa". Imam Ali (a.s) ya ce a cikin Nahjul Balagha: "Ku mayar da dutse daga inda ya fito". Tun daga ranar farko masu neman sauyi a duniyar Musulunci suka bayyana cewa dole ne a kawar da wannan cutar dajin. Imam Khumaini (r.a) ya ce dole ne a kawar da wannan gwamnati daga fage, kuma mafi karancin abin da za a iya yi shi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu ta siyasa da tattalin arziki da wannan kasa mai yin kisa.

Limamin Juma'ar Tehran ya kuma ce: ayarin Sumud ya cancanci yabo, wanda ya hada da jiragen ruwa sama da 70 daga kasashe 44 na duniya da kuma halartar daruruwan masu fafutuka na duniya, wannan hadin kai ne da ya ketare kan iyaka kuma wajibi ne a yaba masa.

Dangane da zarge-zargen da aka yi a cikin sanarwar ministocin kungiyar kasashen Larabawa dangane da tsibiran Iran guda uku, Ayatullah Khatami ya ci gaba da cewa: Ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Larabawa sun sake nanata tsoffin maganganunsu, ina mai gaya musu cewa: tsibiran guda uku na Iran ne kuma sun kasance kuma za su ci gaba da kasancewa haka, wadannan zarge-zarge wasa ne da gwamnatin Sahayoniya da Amurka ke yi, gwamnatin sahyoniyawan tana da'awar samuwar babbar kasar Isra'ila, da kuma son mamaye dukkan kasashen wadannan gwamnatoci, Amma kowanen su ya sani kasar Iran ba makiya ba ce ga makotanta. Amma mu ba zamu yi watsi da kasarmu ba".

Dangane da batun kasar Labanon kuwa, Ayatullah Khatami ya ce: Kwace makaman Hizbullah yana da matukar hadari, ba ga kasar Labanon kadai ba, har ma ga al'ummar musulmi, kuma Hizbullah a kasar Labanon za ta karya lagon wannan mahaukatan sahyoniyawan, ina ce wa gwamnatin Labanon: Sun yi kuskure matuka, Hizbullah ita ce babban hannun Lebanon, kuma wajibi ne su yi amfani da wannan dama.

A cikin hudubar tasa, Ayatullah Khatami ya kuma yi tsokaci kan shawarar da Jagora ya bayar a baya-bayan nan na ba da labarin abubuwan da suka shafi karfin kasar, yana mai cewa: "Kasarmu tana da abubuwa da yawa na karfi da suka hada da 'addini' wanda muke gani karara, da kuma hadin kai da hadin gwiwa, wadanda suke a fili kamar rana, Amurka da gwamnatin sahyoniyawa sun kawo mana hari ne domin mutane su fito kan tituna sun masu in amincewa da hukuma sai dai basu samu nasara ba, to tabbas ina bayar da shawara ga kowa da kowa kan riko da kiyaye wannan hadin kan.

Ya kara da cewa: "Wani bangare na karfinmu shi ne, samuwar jagoranci mai imani da jarumta, kamar yadda duniya ta ga irin ayyukan da ya yi a wannan yakin, a karshe Trump ya daga hannu ya mika wuya ya kuma nemi a tsagaita bude wuta. Wani tushen karfin mu shi ne 'dangantakar mutane da tsarin Musulunci, wanda ke fusatar da makiya, kuma ba za su iya raba mutane da tsarin ba, wani tushen karfin mu shi ne (Karfi Soji) da karfin wajen makami mai linzami, da jirage yaki,da karfin kariya wanda wasu daga cikinsu muka gani a cikin Harin Alkawarin Gaskiya, bayan yakin duniya na biyu, Iran ita ce mai karfi da ikon na farko wajen mayar da martani ga Amurka da kuma karya ikonta. Kuma tabbas Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce, ba za mu bari wani ya yi tattaunawa a wannan fannin ba, ga kuma ‘ci gaban kimiyya' a fannoni daban-daban, ciki har da nanotechnology, sararin samaniya da sauransu.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha